An Kama Jami’an Sojoji Da Na Yan Sanda Da Suke taimakawa ‘yan Boko Haram


Kakakin rumdunar sojojin Nijeriya, Kanal Sani Usman Kukasheka ya bada sanarwar kama mutane 32 wadanda ke da hannu wajen tarayya da kungiyar Boko Haram.
Daga cikin mutane talatin da biyun da aka kama, an sami manyan jami’an sojoji guda biyu, da kuma kananan sojoji biyu, sannan kuma da ‘yan sanda biyu, sai kuma fararen hula guda 26, wadanda yanzu haka suna hannun jami’an tsaro.
A kokarin da rundunan sojojin suke yi na ganin sun yaki ta’addanci a yankin Arewa maso gabashin kasar nan, Rundunar sojojin ta kuma roki al’umma da su kai rahoton duk wani shige da ficen da ba su aminta da shi ba.

You may also like