Rundunar Sojan Nijeriya ta kama daya daga cikin kwamandojin Boko Haram a gidan Shugaban riko na karamar hukumar Mafa da ke jihar Borno, Alhaji Shettima Lawan Maina.
Wata majiyar tsaro ta nuna cewa rundunar Sojan ta kai samame gidan ne bayan ta samu tsegumin cewa Shugaban karamar hukumar ya boye wani dan Boko haram a gidansa da ke rukunin gidajen gwamnati da ke kan titin Maiduguri zuwa Kano inda a halin yanzu ake ci gaba da gudanar da bincike a kan mutanen biyu.