An Kama Magidanci Yana Cire Sassan Jikin Gawa A Makabarta A Jihar Kebbi Jami’an ‘yan sanda dake unguwar Ka’oje, a karamar hukumar Bagudo a jihar Kebbi sun kama wani magidanci dan shekara 37 mai suna Danbaba Umaru yana kwakule wasu sassan jikin wata gawa a makabartar yankin.

Danbaba dai ya kan yi haka ne domin sayarwa ga matsafa wadanda sune sukan tura shi.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi, Ibrahim Kabiru, ya ce sun kama Danbaba ne bayan samun bayanan sirri a kan yana aikata hakan.
Ya ce, Danbaba ya sanar wa ‘yan sandan cewa wani ne mai suna Muhammad mazaunin jihar Sakkwato ya aike shi da ya samu masa wasu sassan mutum.
Danbaba ya ce wannan shine karonsa na farko da ya aikata hakan.

You may also like