An kama mai barazanar kifar da gwamnatin Buhari


 

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya ta bayyana Jones Abiri da aka fi sani da Janar Akotebe Darikoro daga yankin Niger Delta a matsayin mutumin da ya yi barazanar kifar da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tare da kai harin bam a fadarsa da ke Abuja.

An dai kama Darikoro ne a Yenagoa da ke jihar Bayelsa yayin da hukumar ta DSS ta bayyana shi a matsayin shugaban wata hadakar kungiya mai fafutukar neman ‘yancin Niger Delta.

Hukumar ta kara da cewa, mutumin ya amsa laifin aikata manyan laifuka da suka hada da kaddamar da hare-hae kan bututun kamfaninonin man fetir, abinda ke jefa tattalin arzikin kasar cikin mawuyacin hali.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like