Sojojin Najeriya dake aikin samar da tsaro a cikin kasa da aka tura kan babbar hanyar Akwanga dake jihar Nassarawa a ranar Laraba 10 ga watan Janairun 2018, sun kama wani mutum mai suna, Muhammad Bello, da ake zargi da safarar bindigogi kirar gida a cikin wata mota kirar Vectra.
Bello na kan hanyarsa ne ta zuwa saminaka domin haɗuwa da shugabansu da ake kira Damina Saminaka.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya Sani Usman Kukasheka yafitar.
Yace binciken farko ya nuna cewa mutumin da ake zargi yayi ikirarin cewa shima ya sayo bindigogin ne kan kuɗi ₦30,000 a hannun wani maƙeri dake kera bindiga mai suna Dan’asabe Audu, wanda ke zaune a ƙauyen Angbo a ƙaramar hukumar Wamba ta jihar Nassarawa.
“Jajircewar da rundunar tayi wajen gano bakin zaren yasa ta ziyarci ƙauyen inda ta gano cewa eh lallai Dansabe ya dade yana gudanar da sana’ar kera bindiga,” yace.
“An gano cikakkiyar masana’antar ƙera bindiga tare da kayayyakin aiki da kuma bindigogi dake kan matakin kammalawa daban-daban.
“Musanman, sojoji sun gano bindigogi guda uku da aka ƙera da kuma wasu guda 20 dake kan matakin kammalawa daban-daban, kwanson harsashi guda 7, injin huda karfe guda ɗaya, injin bada wutar lantarki da kuma wayoyin hannu guda uku,”
Mai magana da yawun rundunar yace za a mika mutanen ga hukumomin da abin ya shafa domin cigaba da bincike da kuma gurfanar dasu gaban kotu.