An kama mai sayar da sassan jikin mutane a garin Nnewi dake jihar Anambra


 

map-300x295

Yan ƙungiyar sintiri dake garin Nnewi a jihar Anambra sun kama wani mutum da ake zargi da safarar sassan jikin bil’adama a dajin Ukunu Eziora Ozubulu dake ƙarama hukumar Ekwusigo dake jihar.

Shedun gani da ido sunce mutamin wanda ba a  bayyana sunansa ba ankama shine da hadin gwiwar mafarauta da kuma jami’an sintiri dake yankin.

Bayanai sun nuna cewa karnukan  mafarautan ne suka gano sassan jikin biladama adajin da suka hada da hannu, kafa da kuma gangar jikin ba tare da kai ba.

Wannan yasa mafarautan suka sanar da jami’an kungiyar sintiri ta garin Ozubulu, wadanda suka yiwa dajin dirar mikiya, bayan cikakken bincike a dajin sun gano mutumin kuma suka damƙa shi hannun jami’an tsaro.

Bincike yanuna cewa mutumin yana da wani wurin bauta a cikin dajin inda mutane masu bukatar sassan jikin biladama suke zuwa don siya.

You may also like