An Kama Makaman Yaki Da Aka Shigo Da Su Daga Amurka



Hukumar kwastam ta ƙasa da ke kula da gabar teku ta Tin can Island a Legas ta kama wata kwantaina dauke da makaman yaƙi da ake ƙokarin shigowa da su cikin ƙasar daga Amurka.
Hukumar ta ce ta kwashe tsawon kwanaki tana gudanar da bincike kuma sakamakon sa ta gano manyan bindigogi biyu ƙirar Pump Action da dubban harsasai da sauran kayayyakin yaƙi.
Wani babban jami’in hukumar a Legas Bashir Yusuf ya ce an shigo da kwantaina ne daga Amurka, kuma an kama mutum daya da ake zargin yana da hannu a lamarin kuma tuni aka mika shi ga hukumar tsaron farin kaya wato SSS.
Wannan ne karo na biyar a ‘yan shekarun nan da reshen hukumar mai kula da gabar teku ta Tin can Island a Legas ke kama makamai da ake ƙokarin shigowa da su cikin kasar.

You may also like