An kama masu farautar kura a gandun dajin Yankari dake jihar Bauchi


Hausawa suka ce rana dubu ta barawo  rana daya tak ta mai kaya, haka ce ta faru da wasu mafarauta bayan da jami’an kula da gandun dajin Yankari dake jihar Bauchi suka kama su.

Mafarautan sun shiga hannun jami’an tsaro dake yaƙi da yin farautar a dajin  lokacin da suke bin sahun kura domin zuwa wurin da suke taruwa.

Mutanen biyu sun kware wajen kama kura inda suke sayar da ita ga masu wasa da kura ko kuma masu magunguna gargajiya.

Za a miƙa mutanen gaban kotu su fuskanci sharia da zarar an kammala bincike.

You may also like