An kama masu rawa a masallaci a Masar | Labarai | DWA cikin faifan bidiyon, ana iya ganin wani mutum yana tika rawa da tsalle da rera waka da makurufon a cikin masallaci yana bibiyar wakar wani fitaccen mawaki mai suna Ahmed Moza.

Dama dai hukumomi a Masar sun haramta aamfani da irin tsigar wakokin da mutanen suka bibiya, inda ake wa wakokin kallon na banza. Yanzu haka dai mai gabatar da kara ya ce an fara gudanar da bincike kan faifan bidiyon.

“‘Yan sanda sun yi nasarar zakulo wadanda ake tuhuma guda uku, wanda ke rera waka da rawa, da wanda ya dauki hoton bidiyon da kuma wanda ya yada bidiyon a shafukan sada zumunta,” inji wata sanarwa.

Mona Seif, ‘yar uwar daya daga cikin mutane da aka kama mai suna Alaa Abdel Fattah, ta ce jami’an tsaron kasar sun yi wa mutanen uku tambayoyi. Sun fuskanci tuhume-tuhume na “ta’addanci” da ” yada bayanan karya”, in ji mai fafutukar a wani sakon da ta wallafa a Facebook.

Ana yin Allah wadai da kasar Masar a kai a kai kan “mummunan halin da take ciki na zargin cin zarafi da take hakkin bil Adama tun bayan da Shugaba Abdel Fattah al-Sisi ya hau kan karagar mulki a shekara ta 2013.

Kimanin fursunonin siyasa 60,000 ne ke tsare a gidan yari a Masar a halin da ake ciki, a cewar masu kare hakkin bil adama. Masu nishadantarwa masu zaman kansu su kan yi korafin cewa ana fuskantar matsin lamba ko kuma kasa samun masu daukar nauyin a kasar da gwamnati ko rassan jami’an tsaro ke kula da kamfanonin nishadi.

A watan da ya gabata, an saki wasu ‘yan wasan barkwanci uku bayan shafe sama da wata guda suna tsare bisa zargin “bayanan karya” da “ta’addanci” bayan sun buga wata waka a TikTok suna yin Allah wadai da hauhawar farashin kayayyaki da aka yi ta yadawa a Masar.You may also like