Hukumomin tsaro a jihar Filato sun kama wasu mutane da suka hada maza da mata da ake zargi da safarar jarirai.
An dai kama mutanen ne a Jos babban birnin jihar cikinsu har da wata mai ciki da ke gab da haihuwa.
Hukumomi sun ce mutanen da aka kama sun hada da ‘yan mata da akan yi wa ciki su haihu domin sayar da jariran da kuma wasu maza da ake zargi da ajiye ‘yan matan suna yi musu ciki.