An Kama Masu Siyar Da Mushen Nama A Sokoto Kwamitin kula da kayyade farashin abinci wanda karamar hukumar Sokoto ta Arewa karkashin jagorancin Hon. Aminu Ibrahim No Delay Chairman Sokoto ta Arewa ya assasa, karamin kwamiti mai kula da shige da fice naman da ke babbar mahautar Sokoto, ya kama wasu masu sayar da naman mussai a mahautar. 
Da yake na shi jawabi Honarabul Aminu Ibrahim No Delay, yace wadannan ba su ne karo na farko da kamawa ba, ko kwanan baya an kama wasu kuma tuni an hukuntasu suna gidan yari, haka su ma wadannan hukuma za ta hukunta su kamar yadda ya kamata. 
Haka kuma hukuma za ta ci gaba da kula don kiyaye abincin da al’umma ke ci. 
Ya kara da cewa, thohuwar Gwamnatin jihar Sokoto tuni ta gina babbar mahauta ta jiha, inda yake kira ga al’umma da su daina amincewa da duk wata dabba da aka yanka ba bisa ka’ida ba, a kuma daina ci da sayen nama barkatai ba tare da an san tabbacin inda naman ya fito ba.

You may also like