An Kama Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Kaga Bisa Zargin Tallafawa BokoHaramKwamandan Rundunar Sojan Nijeriya na shirin ‘ Zaman Lafiya Dole’ Manjo Janar Lurky Irabor ya  tabbatar da cafke Mataimakih Shugaban Karamar hukumar Kaga da ke jihar Borno bisa zarginsa da tallafa wa mayakan Boko Haram.
Wannan kame dai na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar ta tabbatar da cafke Shugaban Karamar Hukumar Mafa, Shettima Lawan  da Mahaifinsa bisa zargin cewa suna daga cikin masu tallafawa mayakan Boko Haram.

You may also like