An Kama Mutane 3 Bisa Zargin Kisan Gillar Ƙauyen Birane A Jihar Zamfara


Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta sanar da nasarar kama wasu mutane 3 da ake zargi da hannu a kashe kashen da aka yi na fiye da mutane 30 a kauyen Birane da ke karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

Wadanda aka kama din dai sune, Halilu Garba, mai shekaru 45, wanda aka fi sani da Mabushi, sai Zubairu Marafa, shi ma mai shekaru 45, da ake yi wa lakabi da Wakili, sannan da Nafi’u Badamasi, dan shekaru 40, da ake cewa Zakiru.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya, NAN, ya rawaito cewa, ana zargin ‘yan bindigar wadanda ke kashe mutane da satar dabbobi, sun kashe wasu mutane 18 a ranar 14 ga watan nan, a kauyen Birane.

Babban Sufeton ‘yan sanda na kasa, Ibrahim Idris ya kai karin rundana uku ta jami’an kwantar da tarzoma zuwa yankin.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta kasa CSP Jimoh Moshood, ya bayyana cewa ana tsare da wadanda ake zargin, kuma za a cigaba da bincike, kafin a tura su kotu.

You may also like