An kama mutane biyar a kasar Indiya da Laifin dukan wani dan Najeriya


Yan sanda a, Delhi babban birnin kasar Indiya sun kama mutane biyar biyo bayan bullar wani fefan bidiyo dake nuna wasu mutane suna lakadawa wani bakar fata dan Najeriya dukan kawo wuka.

Sun kuma kama dan Najeriya wanda mazauna yankin suka zarga da laifin sata.

Fefan bidiyo ya nuna mutane huɗu ko biyar dauke da sanduna suna dukan wani mutum bakar fata daure a jikin falwaya.

An samu yawaitar hare-hare kan yan Afirka bakaken fata a shekarar da ta wuce ciki har da kisan da aka yi wa dan kasar Kongo ta hanyar lakada masa duka a birnin Delhi.

Yan sanda sun ce wannan abun da yafaru na baya bayan nan ya faru ne ranar 24 ga watan Satumba an kuma kama dan Najeriyar da aka daka saboda zargin sa da laifin sata.

Wani mazaunin unguwar Savitri Nagar shi ne yayi ikirarin cewa mutumin ya shiga cikin gidansa inda yayi kokarin satar masa wasu kayayyaki masu muhimmanci, yan sandan suna ce.

You may also like