An kama mutane biyu suna shirin sayar da motar sata


Yan sanda masu bincike na sashen binciken manyan laifuka na jihar Lagos,sun kama wasu mutane biyu da ake zargin yan fashi da makami ne lokacin da suke kokarin sayar da wata motar da suka sato.

Mutanen da ake zargi Emeka Eze da Okwuduli Emmanuel an kama su ne babbar kasuwar kasa da kasa dake Alaba.

Kwamishinan yan sandan jihar Legas,Imohimi Edgal, wanda ya nuna mutanen ga yan jaridu ya ce jami’an hukumar ne suka kama mutanen a ranar 31 ga watan Mayu.

Edgal ya ce tawagar yan sanda sun samu bayanan sirri kan mutanen daga wani ya boye sunansa.

Sun tsayar da motar akan babban hanyar Badagary kusa da Mile 2 inda suke shirin sayar da motar.

Bayan yi musu tambayoyi mutanen sun amince da sato motar da ma wasu motocin na daban-daban.

You may also like