An kama mutumin da ya kara motarsa a ƙofar shiga hanyar Fadar Gwamnatin Birtaniya



.

Rundunar ƴan sanda a Birtaniya ta cafke wani mutum bayan da wata mota ta bugi ƙofar shiga hanyar Fadar Gwamnatin Birtaniya – Downing Street.

Rundunar ta ce an kama shi ne saboda zargin yin ɓarna da kuma tuƙin ganganci.

Zuwa yanzu dai babu rahoto kan wani da ya jikkata kuma ana ci gaba da bincike, in ji ƴan sanda.

Tuni dai ƴan sanda suka rufe Whitehall – babbar hanyar da ke bi ta Downing Street.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like