Jami’an tsaron sirri na DSS sun bayyana tabbacin kama shugaban tsagin Boko Haram Abu Musab al-Barnawi.
Babban jagoran kungiyar da ISIS ta turo Najeriya don ya maye gurbin Shekau. Wanda aka jiyo suna da musayar yawu da kuma wuta tsakanin sa da Shekau. Kuma na uku a jerin manyan ‘yan ta’adda da Amurka ke nema.
Wanda ya jagoranci kaso da yawa na garkuwa da fararen fata da wasu ‘yan Najeriya a shekarar 2012 zuwa 2015. Wanda gwamnatin Najeriya ta ayyana a matsayin wanda ta ke nema ruwa a jallo a watan Agusta.