An Kama Wanda Ya Kashe DSP Alkali A yayin Zaben Jihar Rivers 



Rahotanni daga birnin Fatakwal sun ce, jami’an rundunar ‘yan sanda sun kama daya daga cikin wadanda ake zargi da kashe mataimakin sufritandan ‘yan sanda Muhammad Alkali lokacin da yake amfani da wayar marigayin.
Bayanai daga cibiyar ‘yan sandan da ke birnin Abuja sun ce, mutumin mai suna Christian Chukwuemeka, na ci gaba da bayar da bayanai ga jami’an ‘yan sandan da ke gudanar da bincike bayan ya amsa zargin da ake masa na kashe DSP Alkali da mai kula da shi Sajen Peter Uchi.
Tuni Chuemeka ya bayyana sunayen abokan aika- aikan nasa guda 9, yayin da jami’an ‘yan sandan ke ci gaba da gudanar da ayyukansu.
‘Yan bangar siyasar dai sun kashe jami’in ne a lokacin gudanar da zaben ‘yan majalisu a jihar Rivers bayan sun yi masa kwantar bauna a Omoku da ke karamar hukumar Onelga in da suka sare kansa.
Jihar Rivers ta yi kaurin suna wajen tashin hankali a lokacin zabe, kamar yadda aka gani a zaben shekarar 2015 da kuma zaben cike gurbin da ya kasa kammaluwa saboda hare-haren da suka kai ga kisan jami’in zabe da masu kada kuri’a.

You may also like