An kama wani bafulatani da rigar sulke a jihar Benue


Sojoji dake sintiri sun kama wani bafulatani da rigar sulke ƙirar gida a ƙauyen Chegba dake karamar hukumar Logo ta jihar Benue.

Aliyu Yusuf wani soja mai muƙamin kanal ya ce mutumin da ake zargi an kuma same shi da adda inda aka miƙa shi hannun  ƴan sanda.

Yusif ya ce ya yin sintirin sojojin sun samu nasarar shiga tsakanin wani mummunan rikici tsakanin makiyaya da kuma wasu mafarauta a ƙaramar hukumar Obi bayan kiran kai daukin gaggawa da suka samu.

A wani cigaban kuma Yusuf ya ce sojoji da suke gudanar da atisayen da ake kira “Gudun Mage” sun samu nasarar ƙwace bindiga ɗaya da kuma harsashi a ƙauyen gidan ƙaya dake karamar hukumar Ibbi ta jihar Taraba.

You may also like