An kama wani fasto ɗan Najeriya da laifin safarar ƙwaya a ƙasar Zambia


Hukumomin Ƙasar Zambia sun tsare wani fasto ɗan Najeriya kan zargin safarar wata ƙwaya dangin hodar ibilis  mai suna ephedrine dake da nauyin kilogiram 26.9.

Isaac Amata mai shekaru 42 ya shahara a ƙasar ta Zambia musamman bayan da yayi hasashen cewa shugaban kasar na yanzu Edgar Lungu shine zai lashe zaɓen ƙasar da aka yi a shekarar 2016.

Jami’an tsaro dake yaƙi da miyagun kwayoyi sune suka kama shi bayan da ya sauka a filin jirgin sama na Kenneth Kaunda dake Lusaka babban birnin ƙasar a cewar, Theresa Katongo mai magana da yawun hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyin ƙasar.

Ta ce faston ɗan Najeriya an kama shine bayan da ya sauka a filin jirgin saman daga Najeriya  cikin jirgin kamfanin jiragen saman ƙasar Afirka ta Kudu.

Ta ce mutamin da ake zargi na hannun jami’an ƴan sanda kuma za’a gurfanar da shi gaban  kotu da zarar an kammala bincike. 

You may also like