An Kama Wani Mai Buga Jabun Kudi A Jihar SokotoHukumar tsaron kasa na fari kaya watau “Nigerian Security and Civil Defense” ta damke wani mutun mai suna Collins Nzewewe, wanda aka samu da laifin buga jabun kudi a jihar Sokoto.
Collins mai shekaru 42 yana da ‘ya’ya bakwai kuma dan asalin kauyen Orlu ne a karamar hukumar Orlu ta kudu a jihar Imo, yace wani Abdulaziz dan kasar Nijar ne ya jefa shi cikin wannan sana’ar.
Collins, wanda mazaunin Sokoto ne ya samu tsawon shekaru uku, a jihar kuma yana sana’ar gyaran babur ne, amma iyalinsa na zaune a can jihar Imo.
Kwamandan jami’an tsaron na farin kaya na jihar Sokoto, Babangida Abdullahi Dutsenma, a lokacin da yake gabatar da shi da wasu tsagera ga manema labarai, yace sun bi sahon mai buga kudin jabun ne bayan da suka samu rahato daga ‘yan kasa na gari da suka tsegunta masu game da harkokinsa.
Ya kara da cewa gabanin damke ‘yan tsageran sai da suka dabawa ma’aikata hudu wuka wadanda yanzu haka suna asibiti ana duba lafiyarsu.

You may also like