An kama wani mutum da kokon kan mutane guda 7 a jihar Kwara 


Wani da ake zargi wanda aka kama da kokon kan mutane guda bakwai na daya daga cikin masu laifin da rundunar yan’sandan  jihar Kwara ta kama a  Ilorin babban birnin jihar.

Kwamishinan yan’sandan jihar,Lawan Ado ya ce,mutumin da ake zargi da aikata laifin an kama shine a kan hanyar Ilorin zuwa Ajaselpo da buhun dake dauke da kokon kan mutane guda bakwai.
 Ya ce mutamin da ake zargin yace ya tono kokunan kan ne daga wata makabartar musulmai dake al’ummar Igbo Owu a karamar Hukumar Ifelodun dake jihar a ranar Talata.

Shugaban yan’sandan ya ci-gaba da cewa mai laifin ya tono kokunan kan ne domin yin tsafi, kuma yan’sanda na cigaba da neman wani mutum guda wanda tare da mutumin da ake zargi suka aikata laifin.

Kana ya kuma ce za gurfanar da mutumin da ake zargi da zarar yan sanda sun kammala bincike.

Yayin da da ake masa tambayoyi mai laifin yace abokin aikinsa da zakara ya bawa sa’a ya tserewa komar jami’an tsaro shine ya saka shi cikin aikata haka, kuma za su yi  amfani da kokon kan guda bakwai domin yin tsafin kuɗi.

You may also like