An kama wani shahararren mai safarar bindigogi da DSS ta shafe shekaru 10 tana farautarsa


Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya, DSS ta ce ta kama Jona Abbey wani shahararren mai safarar bindigogi.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Lahadi ta bakin wani jami’inta, Tony Opuiyo, ya ce an kama Abbey ne a jihar Taraba tare da direbansa mai suna Agyor Saviour.

Opuiyo ya ce Abbey yana sayar da makamai ga gungun batagari dake jihohin Bayelsa, Ebonyi, Rivers, Imo, Anambra, Plateau, Nasarawa, Benue da kuma Taraba.
Jami’in na DSS ya ce Abbey na cikin jerin sunayen mutane da hukumar ta shafe shekaru 10 tana nema ruwa a jallo.

“Idan za a iya lura mutumin da ake magana a kai ya kafa aikinsa a sassa daban-daban na kasarnan kamar yadda aka fada tun da fari, yana da abokan hulda a jihohin Plateau, Ebonyi, Cross River, Enugu and Bayelsa cikin jerin jihohin,” sanarwar ta ce.

“Alamu sun nuna cewa yana samo bindigogin daga kasar Kamaru da kuma Wani bangare na yankin arewa maso gabas


Like it? Share with your friends!

0

You may also like