An kama wani sojan bogi a Lagos


An gurfanar da Victor Nyaku, wani mai gyaran mota a gaban kotun majistire dake Ikeja, a ranar Alhamis inda ake tuhumarsa da laifin sojan gona da kuma cin zarafi.

Ana kuma zargin Nyaku da laifin bayyana kansa a matsayin soja, saka kakakin soja da kuma mallakar katin sheda na yan sanda ba bisa ka’ida ba.

Godwin Awase, dan sanda mai gabatar da kara ya fadawa kotun cewa mutumin da ake zargi ya aikata laifin ne a ranar 14 ga watan Afirilu a Anifowoshe dake Ikeja a jihar Lagos.

Ya ce mutumin da ake zargi, duk da baya aiki da rundunar soja, ya saka kayan soja inda ya bayyana akansa a matsayin babban soja.

“Mutumin da ake zargi yana tuka motarsa kirar Toyota Camry inda ya tare hanyar manyan motocin haya na BRT suke bi inda ya umarci direban da ya yi masa baya domin ya wuce,” ya ce.

“lokacin da direban motar ya gaza yin baya saboda tsayin motar mutumin da ake zargi ya fito da bulala inda ya shiga dukan direban,”

Awase ya cigaba da cewa hakan ne ya jawo hankalin yan sanda dake gefe inda suka zo wurin suka kuma nemi katin shedarsa na aiki amma sai ya nuna musu katin sheda na aikin dan sanda mallakin wani mutum daban.

Mutumin da ake zargin ya amince cewa shi sojan gona ne. Inda ya ce ya samu kakin sojan a wata dilar gwanjo sa da ya sayo daga Kwatano kuma wani mutum ne dake Ikeja ya bashi katin shedar.

Alkalin kotun ya bayar da belinsa kan kudi ₦100,000 da kuma mutane biyu da za su tsaya masa.

You may also like