An kama wani tsohon ministan kasar Kamaru a Najeriya



Atangana Kouna, tsohon ministan albarkatun ruwa da kuma makamashi a kasar Kamaru, an kama shi a Najeriya inda aka tasa keyarsa ya zuwa gida domin ya  amsa tuhuma kan zargin da ake masa na aikata cin hanci da rashawa.

An cire Kouna daga kan mukaminsa bayan da shugaba Paul Biya ya yi wani garambawul ga majalisar ministocinsa ranar biyu ga watan Maris na shekarar 2017 aka kuma umarce shi da kada ya bar kasar cikin watan Faburairu.

“Atangana Kouna yana Kamaru. An kama shi a Najeriya aka kuma tasa keyarsa  a Kamaru ya isa da yammacin nan,” a cewar wata majiyar yan sanda da ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Rueters faruwar lamarin.

Tsohon ministan ya sauka a filin jirgin sama dake Yaounde da karfe 6:30  na yammacin ranar Alhamis bisa rakiyar rakiyar wasu jami’an yan sanda 

You may also like