An kama wasu mata biyu da jariran sata


An kama wasu mata biyu dake da matsaikatan shekaru dauke da jarirai biyu sabuwar haihuwa a wani shingen bincike na sojoji dake Abaji a babban birnin tarayya Abuja.

Wani sheda dake tallan lemon kwalba a shingen binciken ya ce an kama matan ne su biyu lokacin da jamian hukumar yaki da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA suka tsayar da motar da suke ciki.

Ya ce jami’an na hukumar ta NDLEA sun nuna shakku akan matan lokacin da suka yi masu tambayoyi sai suka gaza bawa jami’an jawabi mai gamsarwa.

Wata majiyar yan sanda ta shedawa wakilin jaridar Daily Trust cewa matan daga baya sun bayyana cewa sun sato jariran ne daga wani asibiti dake jihar Abia kuma za su kai wa wani mutum dake Zuba.

Matan sun bayyana cewa an yi musu alkawarin kudi naira dubu talatin idan har suka samu nasarar kai jariran.

You may also like