An kama wasu mutane da jabun sabbin kuɗin NairaJami’an yan sanda dake ofishin yan sanda na Igbo Eze a jihar Enugu sun samu nasarar kama wasu mutane biyu Joseph Chinenye mai shekaru 39 da kuma Onyeka Kenneth Ezeja an shekaru 29 da mallakar sabbin kuɗin Naira na jabu.

Mutanen biyu an same su da mallakar jabun kuɗi na yan naira 1000 har guda 180.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Enugu, Daniel Ndukwe ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa mutanen sun sayo kuɗin ne daga hannu wani mutum dake birnin Benin.


Previous articleWani mutum ya yanke jiki ya faɗi matacce a cikin banki
Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like