An kama wata dalibar jami’ar Maiduguri (UNIMAID) tana kokarin danna wani sabon jariri da ta haifa cikin masai. Bayan ta kashe jaririn nata da kanta, sai kuma tai yunkurin ta batar da jaririn ta hanyar kokarin danna shi cikin masai. Allah cikin ikonsa sai kuma asirinta ya tonu kafin ta kammala mummunan aikin.
Labarin ya afku a dakin kwanan mata mai suna “Murtala Female Hostel”. Har ya zuwa yanzu majiyarmu bata samo mana sunan dalibar da wasu karin bayanai game da ita. Amma ga dukkan alamu dalibar a makaranta ta samu cikin, kuma watakil ba a sani a can gidansu ba. Shi ya sa ta so batar da jaririn a bayan gidan cikin dakunan kwanansu. Allah cikin ikonsa kuma asirinta ya tonu.