An kama wata uwa dake shirin sayar da jariran ta yan tagwaye kan kuɗi ₦350,000 



Wata mace mai shekaru 30, an kamata a jihar Katsina lokacin da tayi yunkurin sayar da jariranta yan biyu mata dake da kwanaki 32 a duniya.
Matar mai suna Salima Lawal da ta fito daga Marabar Ƙanƙara a Karamar Hukumar Malumfashi dake jihar, a cewar kwamishinan yan’sandan jihar, Besen Gwana  tuni ta kammala cinikin sayar da jariran kan kudi ₦350,000.

Yace an kama ta ne bayan da aka tseguntawa rundunar shirin da matar keyi kuma tuni rundunar yan’sandan ta fara gudanar da bincike kan lamarin.

Salma,a zantawar da tayi da manema labarai ta amince da aikata laifin sai dai bata bayyana dalilin aikata  hakan ba.

Amma kuma wata majiyar yan’sanda ta shaidawa wakilin jaridar Daily Trust cewa yayin bincike an gano cewa Salma sun rabu da mijinta wanda suke da daya dan shekara 2.

Ta fadawa masu bincike cewa mijinta,Yusif Abdullahi yana hayar babur ne kuma ya gujeta shi yasa ta aikata haka.

You may also like