Rundunar Sojan Najeriya ta ce wasu zakakuran matasa sun dakile wani harin kunar bakin wake da wata ta yin yunkurin kaiwa a wani masallaci dake garin Gashua a karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe.
Onyema Nwachukwu, mataimakin daraktan hulda da jama’a a rundunar soja ta Operation Lafiya Dole dake aikin samar da tsaro a yankin arewa maso gabas, shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Maiduguri.
“Wata mace yar kunar bakin wake ta shiga masallaci lokacin da mutane suke kokarin fara salla amma aka gano ta lokacin da take kokarin tayar da bom din dake makale a jikinta anyi gaggawar hanata inda aka kama tare da damkata hannun sojoji dake Azare,”ya ce
“Sojojin Operation Lafiya Dole dake yankin da suka kware wajen kwance bom sun samu nasarar kwance bom ya yin da yar kunar bakin waken take karbar magani sanadiyar raunin da ta samu lokacin da aka kama ta.”