An Kamashi Yana Jima’i Da AkuyaHukumar ‘yan sandan jihar Neja ta samu nasarar cafke wani yaro dan shekara 15 mai suna Kabiru Idi bisa zargin yin lalata da akuya.

Hukumar ‘yan sandan ta ce ta samu nasarar ne biyo bayan bayanan sirri da ta samu daga makwabcin wanda ake zargin inda ya kai musu rahoto a ofishinsu da ke Kpakungu a Minna.

Arewa24news  ta samu labarin cewa makwabtan Idi sun ce wannan shine karo na biyu da aka kama Idi yana lalata da akuya. 

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Mista Babolat Adewale ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya bukaci mutane da su kai rahoton duk wani wanda ba su yarda da shi ba wa hukumar ‘yan sanda mafi kusa, sannan ya ce za su mika wanda ake zargin kotu.

You may also like