An Kammala Aikin Kasafin Kudin BanaShugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar Dattawa Sanata Danjuma Goje Ya miƙa bayanan kundin kasafin kudin bana ga Majalisa biyo bayan cece kuce da al’ummar kasa suka yi tayi kan batun batar kasafin kudin bana a gidan Sanata Danjuma Goje wanda hakan ya faru sakamakon samamen da ‘yan sanda suka kai gidan sa.

Yanzu dai ta faru ta kare kundin kasafin kudin bana ya kammalu kuma tuni shugaban kwamitin kasafin kudi ya mika shi ga majalisa.

Shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki ya yabawa kwamitin kasafin kudin bisa namijin kokarin da suka yi wajen sarrafa kundin kasafin kudin na bana daki-daki.

Shugaban majalisar ya kuma jinjinawa kwamitin inda ya ce tun shekarar 1999 rabon majalisa da ta karbi daki-daki na bayanan kasafin kudi tare da kasafin kudin a lokaci guda.

You may also like