An Kara Gano Wata ‘Yar Chibok Dauke Da Jaririnta


 

 

 

Rundunar sojin Nijeriya a jiya Alhamis ta ce ta gano wata yarinya daya daga cikin ‘yan matan Chibok din da har yanzu ake tsammanin suna hannun mayakan Boko Haram.
An gano yarinyar ne yayin da sojojin ofireshon Lafiya Dole ke binciken wadanda suka kama a bisa zargin su ‘yan Boko Haram ne.
An samu yarinyar ne tare da jaririnta dan wata shida a yankin Alagarno a jahar Borno.
Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin Kanal Sani Usman Kukasheka ya fitar ta bayyana cewa binciken da rundunar ta gudanar ya gano cewa yarinyar ‘ya ce ga Abubakar Gali Mulima da Habiba Abubakar dukkansu ‘yan Chibok.
Yarinyar ta bayyana cewa ita ‘yar ajin karshe ce a babbar makarantar sakandire da ke Chibok kafin a sace da tare da abokan karatun ta.
An mika yarinyar ga jami’an kiwon lafiya inda za ta samu kulawa kafin a mika ta ga gwamnatin jahar Borno.
A watan Oktoban da ta gabata ne aka sako wasu 21 daga cikin ‘yan matan na Chibok bayan wata jarjejeniya da aka cimma da kungiyar ta Boko Haram.
Sai dai har yanzu da dama daga cikinsu na hannun ‘ya’yan kungiyar.

You may also like