An Karrama Uwar Gidan Gwamnan Bauchi


Uwargidan gwamnan jihar Bauchi Hajiya Hadiza Muhammad Abdullahi Abdubakar ta samu karramawa ta musamman bisa kokarinta na tallafawa mabukata a taron karramawa ta Zik Prize in Leadership Award 2017 wanda wata cibiya bincike da ake kira a turance Public Policy Research & Analysis Center da ke Lagas ta gabatar mata.

Hajiya Hadiza dai ita ce ya kafa gidauniyar Bauchi Sustainable Women Economic Empowerment & Peace Initiative (B-WEEP). Gidauniyar samar da abin dogaro da kai ga mata da inganta rayuwar kananan yara tare da wanzar da manan lafiya a tsakanin al’uma. Dubban mata da kananan yara a fadin jihar sun amfana da wannan gidauniyar nata tun daga kafata zuwa yau.

Ta kafa gidauniyar B-SWEEP ne domin bunkasa cigaban kasa da zai inganta rayuwar al’uman najeriya na birnin ka karkara, musamman nakasassu da marasa galihu tare da mata a jihar Bauchi.

Shugaban jam’iyar APC ta kasa Cif John Oyegun ne ya gabatar da lambar karramawa ga uwar gidan na gwamnan Bauchi Hajiya Hadiza Muhammad.

Wanda ya dauki wadannan hotuna: Shahruddin Muazu Galaje.

Mun samu wannan sanarwan ne daga Shamsuddeen Lukman Abubakar. Mataimaki na musamman ga gwamnan Bauchi kan al’amuran sanarwa.

You may also like