Akalla mutane 10 aka rawaito sun mutu a wani sabon hari da ake zargin fulani makiyaya da kai wa a jihar Benue.
Jaridar The Cable ta gano cewa maharan sun mamaye wasu al’ummomi dake Saghev a karamar hukumar Guma ta jihar da daren ranar Juma’a.
An ce sun kona gidaje da shaguna kafin su kori mazauna garuruwan.
Moses Yamu , mai magana da yawun rundunar yan’sandan jihar ya ce ba zai iya tabbatar da faruwar kai harin ba.
Da jaridar ta The Cable, ta tuntube shi sai yace “ko labarin kai harin banji ba, yanzu wani ya sanar da ni mintuna kadan da suka wuce. Shine dalilin da yasa nace zan yi magana da jami’in dan sandan dake lura da yankin zan yi maka bayani daga baya.”
Terver Akase,mai magana da yawun gwamnan jihar ya tabbatar da faruwa kai harin akan wasu al’ummomi dake jihar.