An kashe mutane 13 a rikici tsakanin barayin shanu da yan bijilante a jihar Zamfara


Mutane 13 aka rawaito sun mutu a wani fada tsakanin wasu da ake zaton barayin shanu ne da kuma yan bijilante a jihar Zamfara.

An rawaito cewa yan kungiyar bijilante da kuma barayin shanun sunyi musayar wuta a Fakashi, wani surkukin kauye dake gundumar Maru ta jihar daga ranar Talata har ya zuwa Laraba.

Muhammad Shehu, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin.

“Ma’aikatanmu sun gano gawarwaki 13 daga gungun bata garin da kuma yan kungiyar bijilante ta garin, bayan fadan fadan da aka gwabza,” Shehu ya ce.

Barayin ne suka fara kai hari kauyen haka ya jawo mayar da martani daga yan bijilante wadanda galibinsu ke rike da bindiga kirar gida.

Shehu ya ce daga baya an tura karin jami’an tsaro ya zuwa yankin.

Kusan mako biyu da suka gabata wasu yan bindiga sun kai hari kan kauyukan Kabaro da Danmani a karamar hukumar Maru dake jihar inda suka kashe mutane 30.

Kauyukan dake jihar Zamfara sun dade suna fuskantar hare-hare daga yan fashi da kuma barayin shanu hakan yasa kauyukan suke kafa kungiyoyin bijilante domin kare kansu daga irin wadannan hare-hare.

Sai dai a lokuta da dama ana zargin yan bijilante da kashe barayin da suke kamawa ba tare da mikasu ga jami’an tsaro ba.

Ana zargin haka shike haifar da harin ramuwar gayya daga barayi.

Abin jira dai a gani ko yaushe ne hukumomi za su kawo karshen wadannan hare-hare.

You may also like