An kashe mutane 13 a wani rikici tsakanin wasu kungiyoyin asiri dake garin Jos


Wasu kungiyoyin asiri da suke gaba da juna a garin Jos,sun gwabza fada a karshen mako har ta kai ga kisan mutane 13, a cewar wani mazaunin yankin.

Kungiyoyin biyu da ake kira Black Axe da kuma Red Axe a turance sun gwabza faɗa.

Da yake tabbatar faruwar lamarin a ranar Litinin, cikin wata ganawa da aka yi da shi a wayar tarho, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar,Terna Tyopev ya ce an gano gawar mutum guda karkashin wata gadar sama dake kan titin Gudluck Jonathan,Gada Biu karamar Jos North.

Amma kuma mista Tyopev ya gaza bayyana adadin wadanda suka mutum.

“A yanzu dai bani da adadin mutanen da suka mutu amma an gano daya daga cikin gawarwaki karkashin wata gada dake Gadabiu.

Wani mazaunin unguwar Kabang inda rikicin yafaru, Robak Yilji wanda yace an kashe wani makocinsa a rikicin, ya shedawa jaridar premium Times cewa mutane 13 ne suka mutu a rikicin.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like