Hare-haren makamai yayin sanadiyar mutuwar Mutane 46 cikin sa’o’i 48 a kasar Amurka
Cibiyar bincike kan hare-haren makamai a kasar Amurka ta bayyana cewa cikin sa’o’i 48 da suka gabata an kai harin bindiga har so 179 a fadin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar hallaka Mutane akalla 46 tare da jikkata wasu 114 na daban, kuma wasu daga wadanda harin ya ritsa da su matasa ne da kananen yara.
Daga farkon wannan shekara ta 2016 zuwa yanzu, Rahotanni sun bayyana cewa an kai harin bindiga sama da dubu 50 a fadin kasar ta Amurka, harin da yayi sanadiyar mutuwar Mutane kimanin dubu 13 tare da jikkata wasu dubu 27 na daban
Duk da irin kiran da kungiyoyin kare hakin bil-adama da kuma masu kare ‘yan kasa suka yi na a hana sayar da makamai a kasar , har yanzu babu wani matakin da Gwamnatin kasar ta dauka saboda karfin da masu sayar da makamai suke da shi a kasar ta Amurka.