Wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe mutane biyu a kauyen Tsohuwar Gwari dake karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
Wata majiya dake kauyen ta ce yan bindigar sun mamaye kauyen da misalin karfe 12 na daren ranar Asabar inda suka yi garkuwa da mutane shida ciki har da wata amarya.
Ya kara da cewa mutane uku cikin wadanda aka yi garkuwa da su sun samu sun kubuto.
“Sun kashe mutane shida nan take su ka kuma yi garkuwa da mutane 9 duk da uku sun samu sun kubuto,” ya ce.
Aliyu Mukhtar, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna ya tabbatar da faruwar lamarin sai bai yi karin haske ba akai.
Lamarin na faruwa ne kasa da mako guda bayan da aka yi jana’izar wasu sojoji da aka kashe yankin