An kashe mutane uku a wani sabon hari a jihar BenueAƙalla mutane uku aka kashe ya yin da wasu da dama suka jikkata a wani hari da ake zargin fulani makiyaya da kai wa kan ƙauyen Tsokwa dake ƙaramar hukumar Logo ta jihar Benue.

 Nyajo Richard,shugaban karamar hukumar wanda ya tabbatarwa gidan talabijin na Channels faruwar harin,  yace an kai harin ranar Alhamis da daddare.

 Ya ce maharan da ake zargin fulani makiyaya ne sun dirarwa ƙauyen da misalin ƙarfe 8 na dare suna harbi ta ko’ina tare da ƙona gidaje.

Richard ya ce waɗanda suka jikkata a harin yanzu haka suna karɓar magani a asibitin NKST dake ƙaramar hukumar.

An rawaito cewa ƴan sanda sun isa zuwa ƙauyen domin lalubo waɗanda suka ɓace bayan harin.

Logo na daga cikin ƙananan hukumomin da aka kashe mutane a ranar farko ta wannan shekarar.

Harin na zuwa ne ƙasa da sa’o’i 48 baya da rundunar soji ta ƙaddamar da wani atisaye na kwanaki 40 domin kakkaɓe masu kai hare-hare jihohi 6 ciki har da jihar Benue.

You may also like