An kashe mutum guda a wurin zaben shugabannin jam’iyar APC na kananan hukumomi a jihar Gombe


An tabbatar da mutuwar akalla mutum guda a garin Deba dake karamar hukumar Yamaltu Deba ta jihar Gombe lokacin zaben shugabannin jam’iyar APC da aka gudanar a ranar Asabar.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa marigayin mai suna, Salihu Dage, ya rasa ransa ne lokacin wani rikici tsakanin matasa dake biyayya ga bangarorin siyasa daban-daban.

Wani mazaunin garin mai suna,Sani Deba, ya ce bayan marigayin wasu mutane biyar kuma sun samu raunuka a rikicin da ya barke bayan da aka kammala kada kuri’a a zaben na ranar Asabar.

Ya ce wadanda suka samu rauni sun hada da Abdullahi Umar, mai shekaru 28, Abdullahi Puma, Shu’aibu Deba da kuma wasu mutane biyu.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan ta jihar Gombe, DSP Obed Mary Malum, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce an kashe Dage, wasu mutane uku kuma sun jikkata.

DSP Dalum ta kara da cewa rundunar ta kama mutane biyu da ake zargi da hannu a rikicin.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like