An kashe wani da ake zargin bafulatani ne yayin musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaro a Benue


Wani da ake zargin bafulatani makiyayi ne ya rasa ransa lokacin da suka yi musayar wuta da jami’an rundunar yan sanda ta jihar Benue.

Moses Yamu, mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar shine ya shedawa jaridar The Cable faruwar lamarin.

Ya ce lamarin yafaru ne ranar Litinin a Ayilomo wani gari dake ƙaramar hukumar Logo ta  jihar.

“An kashe bafulatanin ne ya yin musayar wuta tsakanin ma’aikatanmu da kuma mutanensa,”Yamu ya fada.

“An samu bindiga a wurinsa, sannan kuma mun kama wani mutum da yake basu bayanai.”

Wannan ne dai karo na uku da ake samun musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da kuma mutanen da ake zargi fulani makiyaya ne dake kai hare-hare akan al’ummomin jihar musamman a ƙananan hukumomin Guma da Logo.

You may also like