An kashe wani makiyayi da shanunsa 15 a jihar Plateau


An kashe wani bafulatani makiyayi da shanunsa 15 a kauyen Rafin Bauna dake kasar Iregwe a karamar hukumar Bassa ta jihar Plateau.
Terna Tyopev,mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar shi ne ya tabbatar da haka ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN,a ranar Talata.

Tyopev ya ce lamarin ya faru da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Litinin.

Ya ce wasu matasa dake garin suma an kai musu haru lokacin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga wurin hakar ma’adanai dake yankin al’ummar Gyero a ranar Litinin.

“Da kusan karfe 5:30 mun samu bayani cewa an kashe wani bafulatani ya yin da 15 wasu yan bindiga da ake zargin mutanen kauyen Iregwe ne suka yanka su a kauyen Rafin Bauna dake karamar hukumar Bassa,” ya ce.

“Har yanzu ba mu gano suna ko kuma adireshin mutumin da aka kashe.

“Haka kuma, wasu matasan Iregwe biyu dake kan hanyarsu ta dawowa daga wurin hakar ma’adanai dake Gyero sun fuskanci hari daga wasu mutane dauke da makamai da ake kyautata zaton fulani makiyaya ne sanadiyyar haka aka sun samu raunuka iri daban-daban.”

Mai magana da yawun rundunar ya ce matasa biyun da suka samu na can ana kula da su a asibitin Enos dake Miangu.

You may also like