Wasu mahara wadanda ba a san ko su wane ne ba sun kashe wani soja a garin Gbeji da ke cikin karamar Hukumar Logo a jihar Binuwai bayan sun yi masu kwantar bauna shi da abokinsa a lokacin suna kan Babur.
Wannan sabon harin dai ya zo ne bayan wani hari da wasu matasa suka kaiwa wani soja a garin Gwer, lamarin da ya harzuka sojojin da aka girke yankin inda suka kona gidaje kusan 30 a garin tare da kashe wani dattijo guda.
A wani labari kuma, wasu maharan sun kai wani hari a wata Gona da ke bayan gidan kurkukun garin Makurdi inda suka arce da Shanu kusan 30. Manajan Gonar, Terwese Uja ya ce maharan sun kai harin ne da misalin Karfe daya na dare inda suka yi harbi a sama da nufin tsorata masu gadin gonar.