An Kashe Wasu Mutane Sanadiyyar Kare Wata Mata Musulma A Kasar AmurkaA Amurka, yanzu haka wasu mutane biyu dake tafiya tare da sauran fasinjoji akan wani jirgin kasa a jihar Oregon, sun mutu, sannan akwai wani mutum na ukku dake kwance a assibiti cikin mummunan hali, duk bayanda suka yi kokarin shiga tsakani a lokacin da suka ga wani mutum yana ta cilla ashar akan wasu mata biyu wadanda, bisa dukkan alamu, Musulmi ne, musamman da yake daya daga cikinsu tana sanye da Hijab.
Shi mutumin da ya nemi cin mutuncin matan, wanda ya dauko wuka, ya shiga sukar sauran mutanen dake cikin jirgin, yanzu haka yana hannun ‘yan sanda, har an bada sunansa da cewa ana kiransa Jeremy Joseph Christian,dan shekara 35, dan garin Portland wanda ashe ma ya taba zama fursuna a gidan wakafi.
A nan take cikin jirgin dai Christian ya soki mutane uku ne, daya ya mutu nan take a cikin jirgin, na biyu ya mutu a asibiti, na ukun kuma ana kulawa da shi a wani asibitin domin ceton ran sa.

You may also like