An kashe yan gudun hijira 7 a jihar Nassarawa


Wasu mutane da ake zargin fulani makiyaya ne sun kashe wasu yan gudun hijira 7 a karamar hukumar Awe dake jihar Nassarawa.

Peter Ahemba, shugaban kungiyar matasan kabilar Tiv dake jihar shine ya tabbatarwa da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN haka.

Yace maharan sun kai wa mutanen harin kwanton bauna a ranar Talata lokacin da suka tafi dauko kayan abinci a kauyen Ihukan.

An ce kowa ya fice daga kauyen sakamakon rikicin dake faruwa a yankin

Ya nuna rashin amincewa da faruwar mummunan lamarin ya yin da yake kira da yan kabilar Tiv da su kwantar da hankali tun da an sanarwa hukumomin da suka dace faruwar lamarin.

Jihar Benue dake makotaka da jihar ta dade tana fama da rikicin tsakanin fulani makiyaya da manoma hakan ya kawo malalar yan gudun hijira ya zuwa babban birnin jihar da kuma jihar Nassarawa me makotaka da ita.

You may also like