An kashe yan kungiyar Boko Haram 411 da kuma  Sojoji 9 a jihar Borno


Hoto:Daily Trust

A kalla yayan kungiyar Boko Haram 411 aka kashe a wani hari ta jiragen sama da aka kai musu a wasu yankuna dake jihar Borno.

Wasu yan farauta da kuma jami’an tsaro na sa kai da ake kira Civilian JTF da ke aiki tare da sojoji a yakin da ake yi da masu ta da kayar baya a jihar Borno, sun   shaidawa wakilin  Jaridar Daily Trust, jiya a Maiduguri cewa an kai harin ta sama ne a wani daji dake kusa da kauyen Gudumbali.

A can dajin ne aka ce masu tada kayar bayan suka shafe makonni suna taruwa inda suka jibge daruruwan yayan kungiyar a sansanoni daban-daban a wani shiri da suke na kai jerin hare-hare.

” Wani jirgin yakin soja ne ya lalata dukkanin sansanoni 6 na kungiyar ta Boko Haram tare da kashe kusan mutane 350,” wani jami’in CJTF ya fada.

A wani wurin na daban a kauyen Musune dake karamar hukumar Dikwa wasu yan kungiyar ta Boko Haram 60 sojoji suka samu nasarar kashewa.

Wani mai gadi a gidan saukar baki na gwamnati dake Dikwa,Malam Harun Ahmad yace ,” a ranar Juma’a sojoji sun yiwa yan ta’addar kwanton bauna inda suka kashe 61 tare da kwato makamai da dama.

A sansanin sojoji dake karamar hukumar Marte sojoji 9 aka kashe bayan da wasu yan ta’adda suka kai hari sansanin da karfe biyar na ranar Alhamis.

Har yanzu dai babu wata sanarwa da ga hukumomin sojoji kan hare-haren. 

You may also like