An kashe ‘yan sanda hudu, 11 kuma sun bace a harin kwanton bauna da aka kai musu a jihar Benue


Jami’an yan sanda hudu aka kashe ya yin da akalla wasu 11 aka bayyana da sun bace bayan da wasu yan bindiga suka kai harin kwanton bauna kan wata tawagar jami’an tsaro a jihar Benue.

Haka kuma maharan sun kona wata motar jami’an yan sandan tare da wasu gidaje ya yin kai harin wanda ya faru lokacin da jami’an su ke gudanar da sintiri daga garin Anyibe zuwa Ayilamo a karamar hukumar Logo ta jihar.

Cikin wata sanawa ranar Litinin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Benue, Moses Yamu ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce tuni babban sifetan yan sandan na kasa ya tura wata tawaga dake bibiyar gungun maharan masu kisa.

Yamu ya bayyana cewa cikin karin jami’an tsaron da aka tura har da masu yawo a jirgi mai saukar ungulu.

Jihar Benue dai ta dade tana fama da rikici tsakanin manoma da makiyaya rikicin da yaki ci yaki cinyewa.

You may also like