An kashe yan’sanda biyu ya yin da aka yi garkuwa da wasu yan ƙasashen waje a Kaduna


Wasu gungun bata gari da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe yan’sanda biyu suka kuma yi garkuwa da wasu yan ƙasashen waje huɗu akan titin Kwoi zuwa  Jere dake karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.

Mutanen sun ziyarci garin Kafanchan da kuma Kaura amma akai musu kwanton bauna akan hanyar su ta dawowa da misalin karfe 7 na daren ranar Talata.

Wata majiyar yan’sanda ta bayyana cewa yan’sandan da aka kashe suna yi wa yan ƙasashen wajen rakiya ne lokacin da aka kai musu harin kwanton baunar.

“Yan’sanda biyu aka kashe a harin ya yin da aka yi awon gaba da ba Amurike daya da kuma wani ɗan ƙasar Kanada a titin Kwoi zuwa Jere idan kabar babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

“Abin bakin ciki ne amma ina da tabbacin yan’sanda za su gano bakin zaren lamarin,” majiyar tace.

You may also like