An kashe yara a harin da matashiya ta kai kan wata makaranta a AmurkaPolice vehicles

Asalin hoton, Reuters

An kashe ƙananan yara uku a wani harin da ake zargin wata matashiya ta kai kan wata makaranta mai suna Covenant School da ke yankin Nashville.

‘Yan sandan Nashville sun ce an gano wadda ta kai harin kuma matashiya ce ‘yar shekara 28.

Haka zalika sun ce harin ya yi sanadin “jikkata mutane da dama”.

Shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar da jawabi a kan harbe-harben na Nashville.Source link


Like it? Share with your friends!

1

You may also like